Dakarun Gaddafi na cigaba da kai hare-hare

Dakarun Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Dakarun Kanar Gaddafi

Dakarun dake biyayya ga Kanar Muammar Gaddafi, sun kaddamar da hari a garin Misrata, mai nisan kilomita 200 a gabashin birnin Tripoli.

Mazauna birnin sun ce tun da sanyin safiyar yau laraba, sojojin ke ta luguden wuta da manyan makaman atilare, a gari na karshe dake hannun 'yan tawaye a yammacin kasar.

Yanzu haka kuma sojojin gwamnati na ci gaba da kai hari a garin Ajdabiyya dake gabashin kasar.