Wani bututun mai ya fashe a yankin Naija Delta

Jami'an tsaro na JTF a Naija Delta Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jami'an tsaro na JTF a Naija Delta

A Najeriya, an sami fashewar wani bututun mai mallakin kamfanin mai na Agip, a jihar Bayelsa ta yankin Naija Delta.

Rundunar gamaiyar jami'an Tsaro na Najeriya, da ke yankin, watau Joint Task Force ta tabbatar da faruwar al'amarin, amma ba ta ce ga musabbabinsa ba.

A kwanakin baya ne dai, kungiyar nan ta MEND, wadda ke ikrarin kare hakkin 'yan yankin na Naija Delta, ta yi barazanar sake ci gaba da kai hare- hare a kan ma'aikatun hakar mai dake Yankin, da ma wasu jihohin kasar.