Nakasassu a Najeriya sun nemi cikakkiyar dama a zabe

A Najeriya alkaluma na nuna cewa akwai nakasassu kimanin Miliyan Ashirin a kasar wadanda sama da Miliyan Goma daga cikinsu sun kai shekarun yin zabe.

Sai dai kungiyar nakasassun na kokawa da cewa da dama daga cikin su ba sa samun damar gudanar da zabuka tamkar yadda sauran 'yan kasar da ba su da nakasa kan samu cikakkiyar damar.

Hakan ta kai ga har sai da kungiyar ta gana da hukumar zaben Kasa mai zaman kanta dan lalubo hanyoyin magance matsalolin da naksassun ke fuskanta a yayin zabuka.

Kungiyar ta yi kira ne ga hukumar zaben Kasar da ta yi musu wani tanadi na musamman a zabukan da ke tafe.