Masu bincike a Kamaru sun gano kwantenoni dauke da makamai

Taswirar Kamaru
Image caption Taswirar Kamaru

A Kamaru, sakamakon binciken da gwamnatin kasar ta umarci jami'an tsaro su yi, kan wasu manyan motocin majalisar dinkin duniya, ya nuna alamar cewa "kwantenoni" 17 daga cikin 40 dake cikin motocin, suna dauke da makamai.

Hakanan kuma wasu karin kwantenonin na dauke da kayan sutura na sojoji da kuma injinan "Janareto".

A jiya ne aikin binciken ya kammala, bayan an fara shi a farkon wannan makon.

Makwanni biyu da suka gabata ne jami'an tsaro na kan iyaka tsakanin Kamaru da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, suka tsare manyan motocin na majalisar dinkin duniya, wadanda aka ce sun fito ne daga kasar Chadi.