Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sauyi ta fanin demokuradiyya a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Najeriya na bukater ababen more rayuwa da kuma farfado da masana'antun da suka durkushe.

A shekarar 1999 ne Najeriya ta sake komawa ga turbar demokuradiyya, a wani lokaci da `yan kasar ke cike da fatan cewa rayuwarsu za ta inganta.

Sai dai bayan sama da shekaru goma sha biyu da komawa ga wannan tafarki, `yan Najeriyar da dama na kukan cewa maimakon demokradiyyar ta kyautata rayuwarsu sai tagayyara suke yi, lamarin da ya cusa `yan kasar cikin tunanin ko zuwa yaushe ne za su samu sauyin da suke fata.

Ibrahim Isa ya yi nazarin irin matsalolin da ke hana demokuradiyya tasiri a Najeriya da kuma hanyar inganta ta. A yi sauraro lafiya.