Kungiyar G7 ta fito da tsarin tallafawa Japan

Ministocin kudi na Kungiyar Kasashen da ke da arziki a duniya bakwai, wato G7 sun bayyana wani tsari na tallafawa tattalin arzikin Japan.

Wannan dai ya biyo bayan yanayin da Kasuwannin Kudi na duniya su ka fara samun kansu, bayan da darajar Kudin Yen na Japan ta yi saman da ba ta taba yi ba a kan Dalar Amurka.

Wannan ne dai karo na farko a cikin shekaru goma da kungiyar G7 ta nemi hadin kai a shiga tsakani game da abinda ke faruwa a Kasuwannin Kudi.

A wani jawabi da ya biyo bayan tattaunawar da su ka yi, Jami'an kungiyar G7 sun bayyana cewa Amurka da Canada da babban bankin Nahiyar Turai za su hada kai domin shawo kan abinda ke faruwa a Japan, a wani yunkuri na su na nuna hadin kai ga al'ummar Japan.

Wannan dai na nufin sayar da kudaden Yen din da suke dasu a ma'ajiyar su domin darajar farashin ta karye.

Wannan jawabin kadai ya yi tasiri nan da nan, inda darajar Yen din ta yi kasa tare kuma da taimakawa wajen daga darajar hannayen jari a kasuwar hada hadar Tokyo.