Ana kokarin gyara tashar nukiliyar Fukushima

Tashar nukiliyar Fukushima Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tashar nukiliyar Fukushima

Ana cigaba da wani gagarumin aikin daidaita al'amura a tashar makamashin nukiliya ta Fukushima a Japan, wadda ta lalace sakamakon mummunar girgizar kasar da aka yi a makon jiya da kuma ambaliyar ruwan Tsunami.

Yanzu dai masu aikin ceto sun fara fesa ruwa a kan tukwanen dake daukar zafi, don sanyaya su ta hanyar amfani da wasu motoci na musamman dake jure wa wuta.

A halin da ake ciki kuma, China ta yi kira ga gwamnatin kasar ta Japan da ta yi cikakken bayani cikin gaggawa, dangane da matsalar dake faruwa.

Tun farko Chinar ta bada sanarwar dakatar da izinin da ta bayar, na bude wasu karin tashoshin nukiliya a kasar, har sai an sake duba ka'idojin kiyaye hadurra a tashoshin, saboda abun da ya faru a Japan.