Majalisar dinkin duniya ta na tattaunawa akan Libya

Sakatariyar  wajen Amurka, Hilary Clinton Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sakatariyar wajen Amurka, Hilary Clinton

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce daukar matakin killace wani yanki na sararin samaniya a Libya zai bukaci yin amfani da kai hari ta sama akan dakarun Gaddafi.

A wani sauyi na kalamai da aka ji, Madam Clinton wadda ta ke ziyara a Tunisia ta ce Amruka tana bukatar kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya amince da kai hari kan tankokin yaki da kuma sojojin kasa na kasar Libya.

Ana sa ran majalisar dinkin duniya za ta kada kuri'a domin neman amincewa da killace sararin samaniyar na Libya.

Rahotanni daga Libyar sun ce sojoji zasu tsagaita bude wuta a ranar lahadi domin baiwa 'yan tawaye wadanda suka ja daga domin kawar da shugaba Gaddafi damar ajiye makamansu.

Kamfanin dillanci labarai na kasar, ya rawaito jami'an soja suna cewa 'yan tawayen zasu iya amfana da wani shiri na yin afuwar gama-gari.