Ba Gaddafi aka kai wa hari ba - Sojin kawance

Hare-Hare kan Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hare-Hare kan Libya

Barkanku da yamma, muna yi muku maraba zuwa shafin BBC Hausa da zai rika kawo muku bayanai kai tsaye dangane da hare-hare da dakarun kawance ke kaiwa a kan sojojin kasar Libya. Bayanan za su kunshi rahotanni daga wakilanmu na sassa daban-daban na duniya a kan rikicin na kasar Libya. Sai ku kasance da mu. Muna kuma marhabin da ra'ayoyinku daga ko ina kuke a duniya. Za ku iya tuntubar mu ta e-mail a hausa@bbc.co.uk, ko ta sakon text a kan lamba +447786202009. Za kuma mu wallafa a bin da ya sawwaka a wannan shafin. Shafin yana sabunta kansa da kansa.

1620:Pira Ministan Burtaniya David Cameron ya ce a yanzu sojojin kawancen suna karkashin gwamnatin Amurka ne, amma ana shirin mayar da batun karkashin More from UK PM David Cameron, who has been saying that the command of the Libya operation will eventually move to Nato: "Let me explain how the coalition will work - it's operating under US command with the intention that this will transfer to Nato," he told parliament. This would mean all Nato allies who wanted to contribute to the mission would be able to. "Clearly the mission would benefit from that and from using Nato's tried and tested machinery in command and control," he said.

1610:Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce Amurkan ta harba karin makamai masu linzami 12 a kan cibiyoyin adana makaman Libiya da kuma wuraren tashin jiragen sama.

1607:Shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma ya shaida wa BBC cewa: "A matsayinmu na Afrika ta Kudu, muna Allah wadai da kisan fararen hula. Ba mu goyi bayan shirin sauya gwamnati ba, kuma ba mu goyi bayan mamayen kasashen waje a Libya ba ko kuma wata kasa mai cin gashin kanta."

1559: Wani mazaunin birnin Tripoli na kasar Libya ya hsaida wa BBC cewa ana ta jin karararrakin bindigogi masu kakkabo jiragen sama a dukkan sassan birnin Tripoli, ya kuma yi Allahwadai da hare-haren da ake kaiwa. "Ya kamata ku yi tunani a kan illar da hakan zai haifar, Ku bar Libya ta ji da kanta. Mu mutanen kirki ne, kuna sanya mu muna fama da wahalhalun da watakila ba za mu fuskanta ba idan da ba ku kawo hari ba.

1558:Fira Ministan Burtaniya David Cameron ya shaida wa majalisar Burtaniya cewa " Ina mai tabbatar wa da majalisa cewa, a yau sojojin kawance sun wargaza makaman yakin sama na kasar Libya, kuma a sakamakon haka mun tabbatar da tsarin hana tashi da saukar jiragen sama a kasar ta Libya.

1556: Shamsuddeen Abdullahi ya wallafa ra'ayinsa ne a shafinmu na BBC Hausa Facebook: Wai shin kasashen yamma sun mata da abin da yake faruwa ne a Ivory Coast? Ko dan ba su da mai ne ko kuma ba kasar Musulmi ba ce? Sai dai Libya? Allah wadarai da kasashen larabawa marasa kishin 'yan uwansu. Kodayake za a mutu a koma ga mahalicci, kowa ya girbi abin da ya shuka.

1550 Lukman Umar Sanyinna ya aiko mana sakon e-mail da ke cewa: Amerika da kawayenta suna kai hari ne domin kwashe man fetur din kasar Libya.

1545:Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wani kakakin 'yan tawaye a garin Misrata yana cewa sojojin da ke biyayya ga shugaba Gaddafi sun yi harbi kan jama'a. Akalla mutane 11 ne suka mutu a harin in ji kakakin 'yan tawayen.

1530: Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato wani kakakin fadar White House a Amurka yana cewa "Sojojin kawance sun ce suna kai hare-hare kan Libya ne domin kare fararen hula, amma ba Gaddafi ake hara ba."