Kungiyar MEND na ikirarin kai hari a Niger Delta

Masu fafutukar MEND
Image caption Masu fafutukar MEND

A Najeriya, rundunar tsaro ta hadin gwiwa a yankin Niger Delta, watau Joint Task Force, ta musanta ikirarin da kungiyar masu faftuka ta MEND ta yi, cewa ita ke da alhakin kai hari kan bututun mai, mallakin kamfanin Agip, a Jihar Bayelsa.

Kakakin rundunar, Laftana Kanar Timothy Antigha, ya shaidawa BBC cewa, suna zargin wani kwamanda ne da ake kira Janar Plasma, da kai harin.

Laftana kanar Antigha, ya kara da cewa da ma Janar Plasma din ya yi barazanar sai ya kai hari a yankin, kuma har yanzu ba su kai ga damke shi ba.

A farkon wannan makon ne kungiyar MEND ta yi barazanar sake kai hare-hare a wasu wurare a yankin Niger Delta.