An bude taro kan kyautata arewacin Nigeria

Nigeria
Image caption Taswirar Nigeria

A Najeriya an bude wani taro na kwanaki 2 a kaduna domin tataunawa a bisa koma bayan tattalin arzikin da yankin arewacin Najeriya ke fama da shi.

Wannan dai taro ne wanda wasu yan yankin suka shirya domin tataunawa da kuma lalubo hanyoyin da zaa warware kuncin talauci da fatara da rashin ayyukan yin dake ci gaba da mamaye yankin Arewa, duk da dimbin arzikin ma'adinai da albarkar kasar noma da yankin ke da shi.

Ana gudanar da taron ne a yayin da ake ta yakin neman zabe a kasar.