Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kulla kawance tsakanin jam'iyyun adawa

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya an dade ana zargin jam`iyyun adawa da kasa yin katabus wajen kalubalantar jam`iyyar PDP wadda ke mulkin kasar cikin shekaru goma sha biyun da ta yi da komawa ga turbar demokuradiyya.

Jam`iyyun adawar dai sun yi yunkuri daban-daban da nufin kulla kawance da juna don tunkarar jam`iyyar PDP, amma ba su kai ga cimma wata kwakkwarar matsaya ba, sakamakon wasu bambance-bambancen da ke tsakaninsu irin na akida da kuma zargin da ake yi wa wasu na son zuciya.

Ibrahim Isa ya yi nazarin kawancen da jam`iyyun adawar ke neman kullawa da kuma kalubalen da suke fuskanta. Ayi sauraro lafiya.