Kwamitin Sulhu ya fitar da kuduri kan Libya

Hakkin mallakar hoto AFP

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da kudurin da ke kira kan garkama dokar haramcin hana zirga zirgar jiragen sama a Libya.

Cikin mambobin kwamitin, kasashe goma ne suka kada kuri'ar su game da daukar wannan matakin.

Babu Kasar da ta ki amincewa da haka, sai dai kasashe biyar basu halarci zaman Kwamitin Sulhun ba, wanda hakan ke nuni da irin banbancin ra'ayin dake akwai a tsakanin mambobin kasashe.

Kasashen Russia da Sin wadanda ke da kujerun dindindin a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ba su yi amfani da damar da suke da ita wajen kada kuri'a ba, sai dai sun kauracewa zaman domin nuna adawarsu da daukar matakin soji.

Jamus da India da Brazil ma sun kauracewa zaman.

Kudurin dai ya tabbatar da saka dokar haramcin hana zirga- zirgar jiragen sama a Libya, tare kuma da amincewa da duk wadansu matakai ciki har da dabarun soji wajen kare al'umar farar hula dake kasar.

Duk da dai wannan bai bayar da damar kasancewar sojojin Kasashen waje zuwa doran kasar ba, sai dai kudurin ya amince da kai hari ta sama idan bukatar hakan ta taso.

Amurka da Birtaniya da Faransa ne dai suka jajirce wajen tabbatar da wannan kuduri.

Can a Kasar ta Libya kuwa, Kanal Gaddafi ya yi alkawarin sake kai hari a wuraren da 'yan adawa suka fi karfi, wato Garin Benghazi.

Ya bayyana cewa za'a bude musu wuta ba bu- sani ba- sabo, muddin suka ci gaba da nuna adawarsu gare shi.

Kanal Gaddafi ya bayyana wadanda ke adawa da shi a matsayin barazana ga Kasar, inda ya kwatanta su da 'ya 'yan karnuka.