Japan ta ja jiki wajen tinkarar matsalar nukiliya

Ma'aikatan nukiliya a Japan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ma'aikatan nukiliya a Japan

Gwamnatin Japan ta amince cewa, ba ta dauki mataki ba cikin gaggawa sosai, bayan mummunar girgizar kasa da ambaliyar ruwan Tsunamin da suka faru a kasar mako guda kenan, wadanda suka janyo matsalar nukiliya.

Japan din ta daga ma'aunin tsanantar lamari daga lamba 4 zuwa 5, a daya daga cikin tashoshin nukiliyarta da suka sami matsala, akan sikelin lamba 7 na kasashen duniya, wanda ke auna matsalar nukiliya.

Matsalar da ake fuskanta a tashar nukiliya ta Fukushima Daiichi, a yanzu tana mataki biyu ne kawai, watau kasa da mummunan bala'in da aka fuskanta a shekarar 1986 a Chernobyl dake Ukraine.

Amma matsalar tana mataki daya da hadarin da ya afku a tsibirin Three Mile a Amurka, a shekara ta 1979.