Gwamnatin Libiya ta daina bude wuta nan take

Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kanar Gaddafi

Gwamnatin Libiya ta bada sanarwar dakatar da bude wuta nan take, a yakin da take yi da masu adawa da mulkin Kanar Gaddafi.

Sanarwar ta zo yayin da kawancen kasashen yammacin duniya da na Larabawa ke shirin kaiwa Libiyar hari ta sama, bayan da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya bada amincewar sa.

Sakatariyar harkokin wajen Amirka, Hillary Clinton, ta ce sun yanke wannan shawarar ce, saboda basu da zabi, ganin irin matakan da Kanar Gaddafi ke dauka.

Ministan harkokin wajen Libiyar, Mussa Kussa, ya ce dole kasarsa ta amince da kudurin Majalisar Dinkin Duniyar, wanda ya hana jiragen sama yin shawagi a sararin samaniyar Libiya.

Tun farko gwamnatin Birtaniya tace nan da 'yan sa'o'i kadan zata tura jiragen yakin ta, domin shirin daukar mataki akan Libiyar.