Sarki Abdullah yayi kashedi ga 'masu tada zaune tsaye'

Sarki Abdullah na Saudiyya Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Sarki Abdullah na kasar Saudiyya yayi gargadin cewa, jami'an tsaro zasu mayar da martani ga duk wani yunkuri na yin makarkashiya ga tsaro da zaman lafiya a masarautar.

A wani jawabin da yayi a gidan talabijin, wanda ba kasafai ya kan yi irinsa ba, sarkin ya yi alkawarin kara baiwa 'yan kasar tallafi.

Ya kuma bayar da sanarwar kafa wata sabuwar hukuma, wadda za ta yaki cin hanci da rashawa.

Bayan jawabin, an kuma bada sanarwar daukar wasu sabbin kudurori a masauratar, inda aka yi alkawarin kara albashi mafi kankanta, da bayar da tallafi ga marasa aikin yi, da inganta tsarin kiwon lafiya da kuma habaka gidaje.