Miliyoyin jama'a sun kada kuria a zaben Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jama'ar kasar Masar

Miliyoyin 'yan kasar Masar sun kada kuri'a a zaben raba gardama kan sauyen sauyen da za'a yi wa kundin tsarin mulkin kasar, makwanni biyar bayan hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Sauye sauyen da sojojin dake mulkin kasar suka gabatar sun hada da kayyade wa'adin mulkin shugaban kasar da za'a zaba nan gaba, da kuma ikon shugaban kasa akan batun daya shafin sanya dokar ta baci.

Wakilin BBC ya ce idan aka amince da gyara kundin tsarin mulkin, sojojin dake mulki na da aniyar gudanar da zabe ne a watan Yunin wannan shekarar.

Sai dai wasu masu rajin kare hakkin bil'adama na ganin yin hakan, an yi gaggawar da zata kawo cikas ga sabbin jam'iyyun siyasar kasar.