Zaben shugaban kasar Haiti

Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Jean Betrand Aristide

Idan an jima a yau ne jama'ar kasar Haiti zasu fara kada kuri'a domin su zabi tsakanin wani shahararen mawakin kasar da kuma matar tsohon shugaban kasar a matsayin shugaban kasarsu.

Sakamakon zaben farkon da aka gudanar a watan Disembar bara ya janyo barkewar tarzoma da aka shafe kwanaki ana yi a kasar, kuma ya sa dantakarar shugaban kasar, me samun goyon bayan gwamnatin kasar shan kaye bayan da jami'an dake sa ido kan zabe suka cire shi bisa zargin magudin zabe.

Yan takarar su biyu da suka tsalake zaben shugaban kasar zagaye na farko mutane ne da suka taba rike mukamai masu muhimanci a kasar.

Sai dai ana ganin tsohon shugaban kasar Haiti, Jean Betrand Aristide zai taka muhimiyar rawa a cikin wanan zabe duk da cewa shi kansa ba zai tsaya takarar shugabancin kasar ba.

Duk wani dantakarar da Mr Aristide ya amince da shi zai shafi tasirin da zai yi a wanan zabe amma idan har ya fadawa magoya bayan sa cewa kada su kada kuriar su a'kan wadanan mutane, hakan zai kara janyo damuwa kan ingancin zaben.