Zaben Najeriya: INEC ta yi karin haske

Image caption Rajistar masu kada kuri'a ta Najeriya

Hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya, wato INEC, ta ba da sanarwar lokutan da za ta gudanar da zabukan kasar a watan Afrilu me zuwa.

Ta kuma jaddada matsayinta a kan jadawalin zabubbukan da ta fitar tun da farko.

Hukumar ta ce masu kada kuria zasu bayyana a rumfunan zabe da za'a kafa da misalin karfe takwas na safe domin a tantance su, a ranar zaben.

Ta ce za'a fara kada kuri'a daga karfe goma sha biyu da rabi na rana kuma sai mutumin karshen da aka tantance ya kada kuri'arsa sanan za'a rufe rumfunan kada kuri'a.

Sai dai wasu jam'iyyun adawar kasar sun bukaci hukumar a'kan ta yi gyara a jadawalin nata, ta yadda za a gudanar da zaben shugaban kasa a karshe, wasu daga cikinsu ma har kotu suka garzaya, amma kotun ba ta biya masu bukata ba.