Wata matsala ta kunno kai dangane da katin zabe a Najeriya

Image caption Shugaban hukumar INEC Farfesa Attahiru Jega

Yayin da ya rage kasa da makwanni biyu a fara babban zabe a Najeriya, yanzu haka wata matsala da ta kunno kai a Jihar Borno ita ce yadda wasu mutane da ake zargi 'yan siyasa ne ke bi, suna saye katinan zabe a hannun jama'a musamman masu karamin karfi.

Wakiliyar BBC a jihar Borno ta ce wasu daga cikin mutanen da suka sayar da katin zabensu sun shaida mata cewa halin kuncin rayuwar da suke ciki, shine ya sa suka yi haka.

Kungiyoyi daban daban da suka hada da na masu sa ido kan harkar zabe a jihar dai na ganin wannan wata hanya ce ta aikata magudi lokacin zaben.

Sai dai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, wato INEC, a jihar Borno, ta bayyana cewar duk wanda aka kama da aikata wannan laifi zai fuskanci hukunci mai tsanani.