Bam ya hallaka mutane biyu a Jos

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, rahotanni daga Jos, babban birnin jahar Plateau, sun ce wasu mutane biyu sun hallaka yayinda suke kokarin tada bam da sanyin safiyar yau.

A cewar wasu rahotanni, mutanen biyu sun yi kokari ne su kai hari a kan wata coci.

To amma jami'an tsaro sun musanta hakan, kuma sun ce suna cigaba da gudanar da bincike.

A farkon wannan watan dakarun tsaro sun gano wata babbar mota, makare da dubban bama-bamai a Jos din.

A 'yan shekarun nan dubban jama'a ne suka rasa rayukansu a tashe tashen hankula a jahar ta Plateau.