Kundin tsarin mulkin kasar Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu kada kuri'a a Masar

Masu kada kuri'a a Masar sun kada kuri'ar amincewa da gagarumin rinjaye bukatar yi wa kundin tsarin mulkin kasar, kwaskwarima da suka hada da kayyade wa'adin mulkin shugaban kasar da kuma inganta harkokin zabe a kasar.

Miliyoyin 'yan kasar ne dai a ranar asabar suka kada kuri'a makwanni biyar bayan juyin juya halin da yayi sanadiyar hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Wakilin BBC ya ce wanan shine karon farko da 'yan kasar da dama zasu kada kuria a rayuwarsu.

Masu kada kuri'a sun ce bai kamata a dakatar da kwaskwarimar da za'a yi wa kundin tsarin mulkin kasar ba.

Sai dai yan adawa na ganin cewa ya kamata a yi wa kundin garambawul gabakidayansa kuma kasar na bukatar karin lokaci domin mika mulki ga farar hula.

Yanzu dai gwamnatin sojin kasar tana shirin gudanar da zabukan Majilisar dokokin kasar nan da wasu watanni kalilan masu zuwa.