Zanga zangar nuna adawa da gwamnatin Syria

Bashar al-Assad, Shugaban Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bashar al-Assad, Shugaban Syria

Jami'an tsaro a Syria sun yi arangama da dubban masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati, a birnin Deraa na kudancin kasar, a rana ta uku a jere.

An ce masu zanga-zangar da suka fusata sun cinna wuta ga gine-ginen jam'iyyar Baath mai mulkin kasar, da kuma ginin wata kotu.

An kashe akalla mutun daya, wasu karin da dama kuma sun jikkata.

Masu zanga-zangar sun yi kiran a sako fursunonin siyasar kasar, a kuma kawo karshen dokar ta bacin da aka kafa yau kusan shekaru 50 da suka wuce.

A ranar Juma'ar da ta wuce ma mutane 4 ne suka rasa rayukansu, a artabun da masu zanga-zanga suka yi da 'yan sanda.