Jakadan Yemen a Majalisar Dinkin Duniya yayi murabus

Ali Abdullah Saleh, Shugaban Yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ali Abdullah Saleh, Shugaban Yemen

Jakadan Yemen a Majalisar Dinkin Duniya, Abdullah al Saidi ya yi murabus.

Yayi hakan ne don nuna rashin jin dadinsa da kisan akalla mutane 50 da dakarun gwamnati suka yi, a lokacin wata zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a Sanaa, babban birnin kasar.

Tun farko ministocin kare hakkin bil'adama da na yawon bude ido sun ajiye aikinsu, tare da shugaban kamfanin dillacin labaran kasar ta Yemen, da kuma jakadan kasar a Lebanon.

Yau dubban jama'a sun fito kan titunan birnin Sanaa da sauran biranen kasar, don halartar jana'izar mutanen da aka kashe.

Sun sake jaddada kiran su na a kawar da shugaba Ali Abdullah Saleh, wanda ya shafe shekaru fiye da 30 a kan karagar mulki.