Wata takaddama ta kunno kai a jami'yyar ANPP

Image caption Malam Ibrahim Shekarau

Rahotanni daga jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya na nuni da cewar an samu wata takaddama tsakanin wasu 'ya'yan jam'iyyar ANPP mai mulki a jihar.

Hakan ya biyo bayan dage babban taron shiyyar arewa maso gabas na yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar, wato Malam Ibrahim Shekarau.

Taron wanda aka shirya gudanarwa a jiya a birnin Maiduguri an dage shi ne saboda gwamnan jihar Borno Ali Modu Sherif ya bayyana cewar bai shirya karbar bakuncin taron gangamin ba.

Ya ce kwamitin yakin neman zaben Malam Shekarau bai bi tsarin da ya kamata ba wajen sanar da shi, lamarin da wasu ke ganin baya rasa nasaba da rashin jituwar da ke faruwa tsakanin gwamnan da takwaran sa na jihar Kano.