Israila ta kaiwa zirin Gaza hari

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Garin Beersheba a Israila inda kungiyar Hamas suka kai wa hari

Israila ta kaddamar da wasu hare hare a Gaza inda aka samu rahotannin fashewar wasu abubuwa har guda tara a wani wuri dake arewacin Zirin Gaza.

Ma'aikatar lafiya a Gazan ta ce akalla mutane goma sha bakwai ne suka samu raunuka wadanda suka hada da kananan yara bakwai.

Wannan harin dai ya biyo bayan harba wasu bindigogin igwa ne daga kudancin Gaza da mayakan kungiyar Hamas suka yi akan Israilar a ranar asabar.

An kuma kaiwa wasu wurare da kungiyar hamas ke samar da horo hari .

Wadanda suka shaida lamarin da idonsu sun ce an kaiwa wani gareji da kuma wata masana'antar simininti hari.

Rundunar sojin Israilar kawo yanzu bata ce komai akan harin.

Hare haren jiragen sama ba wani sabon abu bane a zirin Gaza sai dai alamu na nuni da cewa hari baya baya nan na daya daga cikin hare hare masu karfi tun bayan da Israilar ta kadamar da wani farmaki a Gaza a watan janairun ta shekarar dubu biyu da tara abun da kuma ya yi sanadiyyar mutuwar palasdinawa dubu daya da dari uku.