Jos: Jami'an tsaro sun gano gurin hada bama-bamai

Hakkin mallakar hoto Reuters

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato a Nijeriya na cewa jami'an tsaro sun gano wani wurin hada bama-bamai a birnin wanda ya dade yana fama da tashe-tashen hankula.

Sojoji ne dai sukam kama wasu mutane biyu a kan babur dauke da bom a cikin jakka, daga bisani kuma suka yi wa jami'an tsaron jagoranci zuwa inda ake harhada bama-baman a Unguwar Millonaires Quarters.

Dazu da rana ne hukumomi suka gabatar da wadannan mutane ga manema labarai a birnin na Jos.

A ranar lahadi ne dama wasu mutane biyu suka rasa rayukansu, sa'adda wani bam da suke dauke da shi a kan babur ya fashe.