Jirgin saman soja yayi hatsari a Kano

Shugaban kasar Nijeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban kasar Nijeriya

Rundunar mayakan saman Nijeria ta tabbatar da mutuwar wani hafsanta guda, a wani hadarin jirgin yaki da ya faru yau da rana a Kano.

Sai dai rundunar bata ba da karin bayani ba a kan dalilin faruwar hadarin, wanda ya rutsa da matukin jirgin. Da ma dai shi kadai ne a cikin jirgin a lokacin da lamarin ya faru.