Jirgin Amurka ya fado a Libya

Hakkin mallakar hoto Reuters (audio)
Image caption Jirgin yakin kasashen yamma

Wani jirgin yakin Amurka ya fado a Libya. Mai magana da yawun sojin Amurka ya shaidawa BBC cewa, a ceto matuka jirgin kuma su na cikin koshin lafiya.

Jami'in ya ce ba sojojin Gaddafi bane suka harbo jirgin domin ya samu matsala ne.

Rohatanni da na cewa ana cigaba da gwabza fada tsakanin sojojin Gaddafi da kuma 'yan tawaye a garin Misrata.

Akalla mutane tara ne aka bada rahoton cewa sojojin kanar Gaddafi sun hallaka a Misrata, daya daga cikin biranen da 'yan tawaye ke da karfi.

Bugu da kari a daren jiya litinin an ta jin karar bindigogi masu harbin jiragen sama a Tripoli babban birinin kasar.

Hukumomin Libya sun ce an kaiwa wani sansanin sojin jiragen ruwa da kuma wani kauyen masunta dake kusa da birnin Tripol hari.

A garin Benghazi kuma mutane da dama sun sami raunuka yayinda da wasu sun hallaka.

Duk da cewa gwamnatin Libya ta yi shellar tsaigata wuta kawo yanzu dakarun gwamnati na ci gaba da kaiwa yan tawaye hari a gabashin kasar kuma suna kokarin ganin cewa yankunan da suka kwace sun ci gaba da kasancewa karkashin ikonsu.

Shugaban 'yan tawaye a gabashin Libya ya tattauna da jami'an Majalisar Dinkin Duniya, game da batun kawo agaji ga al'ummar yankin.

Har yanzu dai ana shigowa da abinci ne ta gabashin Libya daga kasar Masar, amma idan yaki a yankin ba takaita ba, alummar gabashin Libya za su fuskanci matsalar abinci.