"Mai yiwuwa yakin basasa ya barke a Yemen"

Ali Abdullah Saleh, Shugaban Yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ali Abdullah Saleh, Shugaban Yemen

Shugaban Yemen, Ali Abdullah Saleh, ya yi gargadin cewa duk wani yunkurin juyin mulki zai jawo yakin basasa a kasar.

Shugaban na magana ne a daidai lokacin da ake ta samun rahotannin karin yawan sojoji da jami'an gwamnati da ke bayyana goyon bayansu ga 'yan adawar dake kiran da ya sauka daga kan mulki. Shugaba Ali Abdullah Saleh ya ce, zai sauka a watan Janairun badi, bayan ya shirya zaben majalisar dokokin kasar.

'Yan adawan kasar sun yi watsi da wannan tayi, suka ce suna son ya bar mulkin nan take.

Rahotanni sun ce wasu sojoji biyu sun hallaka, a fadan da ya hada wasu rukunonin soja masu hamayya da juna, a kudu maso gabashin kasar ta Yemen.