Shugabannin ECOWAS sun soma taro a Abuja

Mata suna zanga-zanga
Image caption Ko taron zai ji kiran matan

Shugabannin kasashen yammacin Afirka na kungiyar ECOWAS ko CEDEAO sun fara wani taro na kwana biyu a birnin Abuja na Najeriya.

Za su tattauna ne a kan abubuwan da ke faruwa a shiyyar, musamman ma rikicin siyasar Cote d'Ivoire da ya ki ci ya ki cinyewa.

Wasu mata sun yi zanga zanga a wajen taron da ake yi a Abujar, suna kira ga kungiyar ta ECOWAS da ta kawo karshen tashin hankalin da ake a Cote d'Ivoire.

Mutane fiye da dari hudu ne suka hallaka, tun lokacin da fadan ya barke, bayan zaben shugaban kasar na watan Nuwamban bara.

Laurent Gbagbo dai ya ki sauka ya ba da mulki ga Alassane Ouattara, wanda duniya ta dauka cewa shi ne ya lashe zaben da aka yi a kasar a watan Nuwamba.