Libya ta yi kiran a dakatar da hare-hare

Jiragen yakin Amurka masu layar zana Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jiragen yakin Amurka masu layar zana

A dare na biyar a jere da dakarun kasashen duniya ke kai hari a Libya, an yi ta jin karar tashin bama-bamai a birnin Tripoli.

Mazauna birnin sun ce ana iya ganin wani bakin hayaki yana tashi a kusa da wani sansanin soji a birnin.

An kuma bayar da rahoton cewa sojoji masu biyayya ga Kanar Gaddafi sun ci gaba da luguden wuta a kan garin Misurata.

Tun da farko dai, kwamandan sojojin saman Burtaniyan da ke kai hari a kasar ta Libya, Air Vice Marshal Greg Bagwell, ya ce a halin yanzu dakarun kawance ne ke iko da sararin samaniyar kasar ta Libya, bayan da suka nakasa rundunar sojin saman Kanar Gaddafi.

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Libya, Khalid Kaim, ya yi kira a kawo karshen hare-haren.

“Hare-hare ta sama ba sa bambancewa tsakanin farar hula da kuma sojoji.

“Saboda haka, domin a samu damar hawa teburin shawarwari kuma rayuwa ta koma yadda aka saba, wajibi ne a dakatar da kai hare-haren nan take”, in ji Mista Kaim.

Mataimakin Ministan ya kuma musanta cewa sojoji masu biyayya ga Kanar Gaddafi suna ci gaba da kai hari a garin Misurata.

Karin bayani