Fargabar aikata magudin zabe a Najeriya

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Farfesa Attahiru Jega, Shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya

A Najeriya, an sha gudanar da zabuka amma a kowanne lokaci ba a rasa zargin magudi daga wadanda suka sha kaye.

Hatta masu sa-ido a kan harkokin zabe kan yi irin wannan zargi na tafka magudi, kuma kusan dukkan jam'iyyun siyasar kasar ne ake zargin cewa duk wadda ta samu wuri takan yi magudi.

Malam Kabiru Danladi Lawanti, wani jami’i a kungiyar kare dimokuradiyya ta Good Governance Group, wanda kuma ya dade yana sa-ido a kan zabuka a Najeriya, ya bayyana cewa kwadayi ne babban dalilin da ya sa ake aikata magudi.

A cewarsa, “Idan [mutum] ya san cewa [sama da fadi da dukiyar al’umma] ba zai yiwu ba, to ba wanda ma zai yi sha’awar dole sai ya yi magudi ya ci zabe”.

Ya kuma kara da cewa hanyoyin magudi suna da yawa, musamman ma a kauyuka inda ’yan jarida da masu sa-ido ba sa shiga.

Dangane da hanyoyin magance magudi kuwa, mai fafutukar kare dimokuradiyyar cewa ya yi: “Matsalar magudi a Najeriya za ta gushe ne kawai idan aka fara siyasa ta manufa—cewa duk wanda ya shiga siyasa, ya shiga ne don ya yiwa jama’a aiki ba don ya je ya arzuta kanshi ba.

“Sannan su talakawan Najeriya su tabbatar da cewa ko wacce mazaba an kai masu rumfar zabensu; bayan haka su tabbatar da cewa kowa ya fito ya yi zabe—su tsaya a wurin su tabbatar da cewa malaman zabe sun kidaya kuri’un kuma a fada masu wanene ya ci zabe a wannan mazabar”.