A Syria an kashe masu kin jinin gwamnati

Masu zanga-zanga a birnin Damascus na Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga a birnin Damascus na Syria

Rahotanni daga birnin Dera’a da ke kudancin Syria na cewa ’yan sanda sun kai hari a kan wani masallaci wanda ya zama matattarar masu kin jinin gwamnati.

Akalla mutane biyar ne dai aka kashe yayin wannan hari.

Kafin ’yan sanda su kai wannan hari dai a safiyar yau din nan, an yanke layukan wutar lantarki da kuma ruwa a yankin.

Tuni dai gwamnatin Syria ta zargi masu zanga-zanga a kasar da kasancewa ’yan koren Isra'ila.

Ranar Juma'ar da ta gabata ne dai aka fara tarzomar neman ’yanci da kuma kawo karshen aikata cin hanci da rashawa a birnin na Dera’a.