Libya ta bijirewa Kwamitin Sulhu -Ban

Jiragen kasashen kawance a samaniyar Libya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jiragen kasashen kawance a samaniyar Libya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya shaidawa Kwamitin Sulhu cewa Libya ba ta aiki da tanade-tanaden kudurin Majalisar.

Mista Ban ya kuma yi gargadin cewa Kwamitin Sulhun ka iya daukar wadansu karin matakai idan kasar ta Libya ta ci gaba da bijirewa bukatun Majalisar.

A wata hira da ya yi da BBC daga bisani kuma, Sakatare Janar din ya nuna damuwa a kan yiwuwar jikkata farar hula yayin da ake ci gaba da daukar matakin soji a Libya.

Don haka ya bukaci kasar ta Libya ta yi biyayya ga bukatun Kwamitin Sulhu na Majalisar, ta dakatar da bude wuta.

Mista Ban ya kuma jaddada cewa manufar harin da sojojin kawance ke kaiwa a kan Libya ita ce kare farar hula ba kawar da Kanar Gaddafi daga kan mulki ba.

To ko a ra'ayin Mista Ban, lokaci ya yi da ya kamata Kanar Gaddafi ya sauka daga mulki?

“Kanar Gaddafi ya riga ya rasa halalcinsa tunda ya karkashe al'ummarsa babu gaira babu dalili”, in ji Mista Ban.

Ya kara da cewa: “Dangane da batun ya sauka ko a maye gurbinsa da wadansu kuwa, jama'ar kasar Libya ne kadai za su iya yanke hukunci.

Da ya ke amsa tambaya a kan ko yana ganin kudurin Kwamitin Sulhu ya baiwa kasashen kawancen damar samarwa 'yan tawaye makamai don su yaki Gaddafi, sai Mista Ban ya ce samar da makamai ga wani baya cikin tanade-tanaden kudurin.

Karin bayani