ECOWAS ta yi kiran amfani da karfi a Cote d'Ivoire

Ministan matasan Cote d'Voire Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya an zargi ministan cikin gida da zuga matasa

Kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO, ta bukaci Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya kara ikon dakarunta majalisar, masu aikin kiyaye zaman lafiya a Cote d'Ivoire.

A cewar ECOWAS din, ya kamata a ba sojojin ikon daukar duk wani mataki da ya wajaba, domin tabbatar da cewa an mika mulki ga Alassane Ouattara, mutumen da kasashe suka yi amunnar shine ya lashe zaben Cote d'Ivoire din na watan Nuwamba.

Shugabannin ECOWAS sun yanke wannan shawarar ce, a karshen taron kwana biyun da suka yi a Abuja.

Kusan mutane dari biyar ne suka hallaka, a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben na Cote d'Ivoire.

Har wayau ECOWAS din ta dage takunkumin da ta sanya ma Nijar da kuma Guinea.