Faransa ta kai hari a kan jirgin saman Libya

Jiragen kasashen yamma Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A karon farko an lalata jirgin Libya guda

Jirgin yakin Faransa ya harbo wani jirgin yakin Libya a karo na farko, tun bayan da kasashen yamma suka fara kai hari a Libya.

Sojin Faransa sun ce an harbo jirgin Libyan ne bayan ya sauka a filin jirgin saman birnin Misrata.

A wajen birnin Misrata kuma rahotanni sun ce an lalata tankunan yakingwamnatin Libya guda biyu a yayin da sauran takunan ke cikin birnin kusa da wani tashar jirgin ruwa.

Gidan talabijin gwamnatin Libya na nuna jana'izar wadanda suka ce harin kasashen yamma ne ya kashe su.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Libya ya ce harin kasashen yamma ya kashe akalla fararen hula dari.

Wani Likita a Misrata ya shaidawa BBC cewa sojojin Gaddafi na ci gaba da kai hari a kan fararen hula.