Za'a shafe makwanni ana kai hare hare kan Libya

Alain Juppe, Ministan waje na Faransa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alain Juppe,

Gwamnatin Faransa ta yi bayani akan nasarorin da ta ce kasashen kawance sun samu, a hare-haren da suke kaiwa a Libya.

Ministan tsaron Faransar, ya ce, ba wai kawai sun hana jiragen saman Libya yin shawagi a gabar tekun kasar ba, a'a, har ma sun nunawa Kanar Gaddafi karara cewa, ba zai yi nasara ba a hare-haren da yake kaiwa jama'arsa.

Shi ma ministan kula da harkokin waje na kasar Faransa, Mr Alain Juppe ya ce za'a karya lagwon sojojin Gaddafi cikin 'yan kwanaki, ko kuma makwanni.

A daren jiya an ji karar fashewar bama-bamai a Tripoli babban birnin kasar. Rahotannin da ake samu na cewar, dakarun Gaddafi na yin luguden wuta a birnin Misrata na yammacin kasar.