Takaddama a kan 'A-kasa-a-tsare-a-raka'

Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega

A Najeriya, bangarorin al'umma da dama sun dukufa wajen ganin babban zaben kasar da ke tafe ya kasance mai inganci.

Hatta shugaban kasar, Goodluck Jonathan, yana cikin wadanda ke da'awar cewa ya kamata 'yan kasar su tabbatar an kidaya kuri'un da suka kada a kan idanunsu a rumfunan zabe.

Su ma 'yan siyasa, musamman bangaren 'yan adawa, sun jaddada muhimmancin sa-ido a kan kuri'un da za a kada.

Sai dai rundunar 'yan sandan kasar ta ce ba za ta bari masu zabe su tsaya kusa da akwatin zabe bayan kada kuri'a ba, sai dai su tsaya daga nesa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mista Olusola Amore, ya shaidawa BBC cewa, “’Yan sanda ba su hana kowa tsayawa ba; amma za su kyale mutane su tsaya akalla tazarar mita dari uku tsakaninsu da rumfunan zabe—haka ne zai baiwa jami’an hukumar zabe damar gudanar da aikinsu a tsanake”.

Tazarar mita dari uku dai ta kai tsawon filin kwallon kafa har sau uku.

Kuma da wuya wannan tazara ta bari a iya fahimtar abin da ake yi a rumfar zaben.

Wannan matsayi na rundunar 'yan sanda ya sanya wasu 'yan siyasa sun fara kokwanto game da gaskiyar dukufar gwamnatin kasar wajen gudanar da sahihin zabe.

Sai dai yayin da rundunar 'yan sandan ke kwadaitawa jama'a tsayawa nesa da wajen da suka kada kuri'a muddin dai za su kasance masu bin doka da oda, shi kuwa mai baiwa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaro, Janar Andrew Azazi, ya bayyana cewa samsam babu wanda zai kasance a wajen jefa kuri'a bayan kammala kada kuri'ar.

Janar Azazi ya shaidawa BBC cewa babu wani sashe a tsarin dokar kasa da ya tanadi jama'a su tsaya a wajen kada kuri'a domin a kidaya kuri'ar a gabansu.

“Umurni na karshe da za mu bayar shi ne duk wanda ya kada kuri’arsa to ya tattara nasa-ya-nasa ya bar rumfar zabe, domin ba ma son duk wani abin da zai haifar da tashe-tashen hankula”, in ji Janar Azazi.

Tuni dai jam'iyyun adawa suka bayyana cewa sun sansano wani shiri na tafka magudi bayan furucin na mai baiwa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaro.

Sakataren jam'iyyar CPC na kasa, Injiniya Buba Galadima, ya bayyana cewa ko da wasa Janar Azazi ba shi da hujjar daukar wannan matsaya.

A cewarsa, “Shi mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro ba shi ne hukumar zabe ba; mu wanda muka sani, wanda zai iya ba da wannan umurni, shi ne Farfesa Attahiru Jega”.