An kashe masu zanga-zanga 20 a Syria

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

Masu zanga-zangar neman sauyi a Syria sun zargi gwamnatin kasar da laifin yin amfani da jami'an tsaro don bude wuta a kan masu zanga-zangar lumana.

Masu zanga-zangar sun kuma ce an kashe akalla mutane ashirin jiya Juma'a a garin Dera'a wanda ke kudancin kasar bayan wani gungun mutane sun kona mutum-mutumin tsohon shugaban kasar, Hafiz Al-Assad.

Yadda shugaban kasar ta Syria da kuma masu ba shi shawara suka tunkari masu zanga-zanga ne kawai zai tantance makomar kasar.

Wadansu kasashen Larabawan da dama ma sun fuskanci zanga-zanga iri-iri.

A Yemen, masu goyon baya da kuma masu adawa da gwamnati sun yi zanga-zanga a babban birnin kasar.

A Jordan ma dai an yi arangama bayan masu goyon bayan gidan sarautar kasar sun jefi masu neman sauyi da duwatsu.

A tashin hankalin na Jordan dai mutum guda ya mutu.

A Bahrain kuma masu neman sauyi ne ke kokarin sake taruwa tun bayan aza dokar ta baci a kasar.