Kwamitin Sulhu ya sawa Gbagbo takunkumi

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Abidjan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Abidjan

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya azawa Laurent Gbagbo sabbin takunkumi, saboda kin mika mulkin Ivory Coast ga wanda kasashen duniya suka yi ittifakin cewa shi ne ya lashe zaben da aka yi bara.

Kwamitin Sulhun ya kuma umurci dukkan bangarorin kasar ta Ivory Coast su amince da Alassane Ouattara a matsayin shugaban kasar.

Da ma dai ana zargin Kwamitin Sulhun da yin baki biyu wajen bayar da umarnin kai hare-hare ta sama domin kare al'ummar Libya, yayinda kuma ya yi ko-oho da tashin hankalin da ake yi a Ivory Coast.

Rahotanni daga kasar ta Ivory Coast sun ce dakarun da ke goyon bayan Mista Ouattara sun shiga garin San Pedro wanda ke gabar teku, inda ake fitar da cocoa zuwa kasashen waje.

Karin bayani