Yanayin tashar Fukushima ya munana

Pira Ministan Japan, Naoto Kan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Pira Ministan Japan, Naoto Kan

Makwanni biyu bayan mummunar girgizar kasa da mahaukaciyar ambaliyar ruwa ta Tsunamin da suka yi muguwar barna a kasar Japan, Piya Ministan kasar, Naoto Kan, ya shaidawa al'ummar kasar cewar yanayin da ake ciki a tashoshin nukiliyar da wannan abu ya shafa yana da muni.

Haka nan kuma ya bayyana ta'azziyarsa ga mutanen da wannan bala'i ya shafa, inda a yanzu aka tababtar da mutane sama da dubu goma sun rasa rayukansu.

Jami'ai a tashar ta Fukushima dai sun ce adadin tururin nukiliya dake cikin ruwan da ke cikin daya daga cikin tukwannen tashar, ya ninka wanda ake bukata bisa ka'ida, har sau dubu 10.

Abun dake nuna cewa wani sashe na tukunyar ya lalace. Sai dai daga bisani Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Japan din ta ce babu wani bayani dake tabbatar da hakan.