Zanga zanga a yankin Gabas ta tsakiya

Masu zanga zanga a Yemen Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Masu zanga zanga a Yemen

Dubun dubatar mutane ne suka fita kan tituna a biranen Sana'a na kasar Yemen da Deraa na Suria, a kokarin da suke yi na samun 'yan cin walwala da bayyana albarkacin bakinsu ba tare da wata fargaba ba.

Masu zanga zanga a birnin Yemen na kira ga Shugaba Ali Abdullah Saleh da yayi murabus ba tare da bata lokaci ba, yayin da masu maci a birnin Deraa na kasar Syria, ke halartar jana'izar mutane ashirin da biyar din da aka bindige har lahira a lokacin zanga zangar da aka yi ranar laraba.

A can ma birnin Damuscus ance an yi wata zanga zangar, inda aka kama wasu mutane.

Shugaba Ali Abdullah Saleh na Yemen, yayi jawabi ga magoya bayansa, inda ya ke yin Allah wadai da zanga zangar, yana mai cewa a shirye yake ya mika mulki cikin ruwan sanyi.