Nuna banbancin addini matsalace ga zabe

Masu zabe a Nigeria
Image caption Masu zabe a Nigeria

Yayin da ake saura kwanaki takwas a fara zabukan Nigeria, wasu Malaman addinin Musulunci da na Kirista sun fara nuna damuwarsu, akan yadda suka ce wasu a kasar suna sanya addini a cikin harkokin siyasar kasar.

Malaman addinan biyu sun yi zargin cewar akwai wadanda ke kira ga mabiyansu daga dukkanin bangarorin da su zabi shugaban da ke bin addininsu, abun da suka ce sam bai da ce ba.

Akan haka ne shugabannin kungiyar kirista ta CAN reshen Jihar Kaduna da kuma shugabannin kungiyar Jama'atul Nasrul Islam reshen kadunan suka gudanar da wani taron manema labarai, inda suka jaddada hadin kai a matsayin abinda zai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da zabe na gari a kasar.