'Yan tawayen Libya sun kwace garin Ajdabiya

'Yan tawaye a garin Ajdabiya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan tawaye a garin Ajdabiya

'Yan tawaye a gabashin Libya sun sake kwace garin Ajdabiya mai muhimmanci sosai daga hannun sojin da ke biyaya ga Kanar Gaddafi.

Shi ne garin farko da ya sake fadawa hannun 'yan tawayen, tun bayan da kasashen Yammacin duniya suka hana zirga-zirgar jirage a sararin samaniyar kasar ta Libya.

Wadanda suka shaida al'ammarin sun ce sun ga tankoki da motocin soja da dama da aka ragargaza ko kuma matukansu su ka gudu su ka bar su.

Rahotanni sun ce yanzu 'yan tawayen suna dannawa yammacin kasar zuwa garin Brega.

Mataimakin ministan harkokin wajen Libyar, Khaled Kaim, ya ce dakarun gwamnatin sun janye ne daga garin bayan da jiragen saman kasashen waje suka dinga kai masu hari.

Ya kuma zarge su da goyon bayan 'yan tawayen kai tsaye.