An yi gagarumar zanga-zanga a London

Masu zanga-zanga a London Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Masu zanga-zanga a London

A yau dubun-dubatar jama'a ne ke yin wata zanga-zanga a tsakiyar birnin London, don nuna adawa da matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka na rage kashe kudade wajen samar da ababen more rayuwa.

Kungiyoyin kwadago suka ce, ana sa ran zanga-zangar za ta kasance mafi girma da birnin na London ya gani tun bayan zanga-zangar da aka yi gabannin kai hari a Iraqi.

Ita dai gwamnatin Birtaniyar ta ce rage kashe kudaden ya zama dole domin a cike gibin kasafin kudin da kasar ta ke fama da shi.