Takaddama a kan sauke wasu shugabannin kananan hukumomi a Plateau

Wani jami'in tsaro a Jos Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jihar Plateau dai ta sha fama da rikice-rikice.

Rahotanni daga jihar Filato na cewa yanzu haka ana tayar da jijyoyin wuya a sakamakon matakin da gwamnan jihar, Jonah Jang, ya dauka na sauke wasu shugabbannin kanannan hukumomi na jam'iyyar adawa ta Labour daga mukamansu.

Gwamnan dai ya ce ya sauke shugaban karamar hukumar Kanam, Barista Saleh Muhammad, da na Langtang ta Kudu, Mista Hitler Dadi ne, saboda baiwa gwamnatinsa damar gudanar da bincike kan zargin almubazaranci da take ma su, amma shugabannin na cewa matakin na da nasaba da siyasa.

Kafin sauke shugabanin kananan hukumomin daga mukamansu, gwamnatin jihar ta dakatar da baiwa kananan hukumomi hudu na 'yan adawa kudadensu na wata- wata daga gwamnatin tarayya wadanda kan bi ta hannunta.