Sabon tashin hankali ya barke a Syria

Masu zanga-zanga a birnin Deraa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga a birnin Deraa

Tashin hankali ya sake barkewa a Syria, bayan an kashe mutane akalla ashirin da biyar a garin Deraa, inda aka yi zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati.

Rahotanni daga birnin Latakia sun ce an yi harbe-harbe sosai, da kuma bude wuta a kan masu zanga-zanga da 'yan kisa daga boye suka rika yi.

An ba da rahoton kisan mutane uku.

Wani mutum da ya shaida al'ammarin, ya ce an yi harbin ne lokacin da taron jama'ar suka far ma ofishin Magajin Gari da kuma mutum-mutumin tsohon shugaban Syriar, Hafeiz al Assad.