Tauttaunawa kan mika mulki a Yemen

Masu zanga-zanga a Yemen Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Yemen

Wani jami'in gwmanati a Yemen ya ce, ana kusa ga cimma 'yarjejeniya a kan yadda shugaba Ali Abdullah Saleh zai mika mulki.

Ministan harkokin waje, Abubakar Al Qirbi, ya ce a shirye shugaban yake ya duba yiwuwar haka, matsawar dai da gaske 'yan hamayya suke yi game da maganar tattaunawar.

Wakilin BBC a Yemen ya ce, wannan ne karon farko da gwamnati ta tabbatar cewa a shirye shugaban yake ya bar mulki.

Shugaba Saleh dai ya ce a shirye ya ke ya sauka a karshen shekara, amma 'yan adawa sun ce so suke ya sauka nan take.