Damuwa kan yawan tururin nukiliya a Japan

Tashar nukiliya ta Fukushima Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tashar nukiliya ta Fukushima

A Japan, kamfanin da ke kula da tashar nukiliyar Fukushima, wadda ta lalace sakamakon girgizar kasa da kuma ambaliyar ruwan Tsunami, ya ce ya yi kuskure wajen bayyana yawan tururin nukiliyar da ke fita, tun farko a yau.

Kamfanin ya nemi ahuwar ce, bayan da ma'aikata suka ranta a na-kare, bayan na'urar gwaji ta nuna cewa, tururin nukiliyar da ke cikin ruwan tashar nukiliyar Fukushima ta biyu, ya ribanya adadin da ya kamata a samu a ruwa, har sau miliyan goma.

A cewar wani mai magana da yawun kamfanin, lallai ruwan ya tabu, amma ba kamar yadda aka bayyana tun farko ba, kuma a yanzu ana kara yin wani gwajin.